1 Timothy 3

Masu Kula da Ikkilisiya da Masu Hidimar Ikkilisiya

1Ga wata tabbatacciyar magana: In wani ya sa zuciyarsa a kan zama mai kula da ikkilisiya,
A alʼadance bishob; haka ma a aya 2
yana marmarin yin aiki mai daraja ne.
2To, dole mai kula da Ikkilisiya yǎ kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa, 3ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba. 4Dole yǎ iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yǎ kuma tabbata cewa ʼyaʼyansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace. 5(In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?) 6Kada yǎ zama sabon tuba, in ba haka zai zama mai girmankai yǎ kuma fāɗa cikin irin hukuncin da ya fāɗo wa Iblis. 7Dole kuma yǎ kasance da shaida mai kyau ga waɗanda suke na waje, don kada yǎ zama abin kunya yǎ kuma fāɗa cikin tarkon Iblis.

8Haka masu hidima a cikin ikkilisiya; su ma, su zama maza da sun cancanci girmamawa, masu gaskiya, ba masu yawan shan ruwan inabi ba, ba masu kwaɗayin ƙazamar riba ba. 9Dole su riƙe asirin bangaskiya su kuma kasance da lamiri mai tsabta. 10Dole a fara gwada su tukuna; saʼan nan in ba a sami wani abin zargi game da su ba, sai su shiga aikin masu hidima.

11A haka kuma, dole matansu su zama matan da suka cancanci girmamawa, ba masu gulma ba, sai dai masu sauƙinkai da kuma masu aminci a cikin kome.

12Dole mai hidimar ikkilisiya yǎ zama mijin mace guda dole kuma yǎ iya tafiyar da ʼyaʼyansa da kuma iyalinsa da kyau. 13Waɗanda suke hidima da kyau suna samar wa kansu kyakkyawan suna da kuma cikakken tabbatarwa a cikin bangaskiyarsu cikin Kiristi Yesu.

14Ko da yake ina sa zuciya zo wurinka nan ba da daɗewa ba, ina rubuta muka waɗannan umarnai domin, 15in na yi jinkiri, za ka san yadda ya kamata mutane su tafiyar da halayensu a cikin jamaʼar Allah, wadda take ikkilisiyar Allah rayayye, ginshiƙi da kuma tushen gaskiya. 16Ba shakka, asirin addini da girma yake:

Ya
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā suna da Allah
bayyana cikin jiki,
Ruhu ya nuna shi adali ne,
malaʼiku suka gan shi,
aka yi waʼazinsa cikin alʼummai,
aka gaskata shi a duniya,
aka ɗauke shi sama cikin ɗaukaka.
Copyright information for HauSRK